Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta san an yi kamu ba

Ginin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja Hakkin mallakar hoto nta
Image caption Ginin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja

Majalisar Dinkin duniya ta ce, a hukumance, Gwamnatin Najeriya ba ta sanar da ita labarin cafke wasu da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai wa ginin Ofishinta da ke Abuja babban birnin Najeriyar ba.

Majalisar dinkin duniyar na mayar da martani ne game da ikirarin da mahukunta Najeriyar ke yi cewar suna tsare da wasu mutane biyu da suke zargi da kitsa kai harin.

A jiya ne hukumar tsaron ciki ta Najeriyar watau SSS ta bayyana kamun mutanen a cikin wata sanarwar da ta fitar a Abuja, sannan kuma ta ce ta na neman wani madugunsu na ukku mai suna Mamman Nur.