Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haifi Ki Yaye da BBC Hausa: Tsabtar yara da muhallinsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yana da kyau a samar da tsaftataccen muhalli ga yara kanana

A wani shiri da majalisar dinkin duniya ta kaddamar kan lafiyar yara da kuma muhallinsu a shekarar 2009, domin taimakawa wajen cimma muradun karni, ya jaddada mahimmancin kula da tsabtar yara da ta muhallin da suke ciki.

Asusun UNICEF tare da hadin gwuiwar hukumar lafiya ta WHO da kuma hukumar kare muhalli ta Majalisar dinkin duniya UNEP sun bayyana cewa tsabtar yara da kuma ta muhallinsu na taka mahimmiyar rawa a bangaren tsabta a duniya baki daya, wanda rashin kula kan janyo gagarumar barazana ga lafiya.

A wani rahoto da hadakar hukumomin suka fitar, na nuni da cewa a duk shekara, kimanin yara miliyan uku a duk duniya 'yan kasa da shekaru biyar ne ke mutuwa a saboda cututtukan da suka shafi muhalli.

Sannan kuma fiye da yara miliyan daya da rabi ne 'yan kasa da shekaru biyar a duniya ke rasuwa a sanadiyyar cututtukan da suka danganci numfashi.

Rahoton ya kuma ce fiye da yara miliyan daya da rabi 'yan kasa da shekaru biyar ne a duk duniya ke rasuwa a saboda amai da gudawa, yayinda kusan yara miliyan daya ke rasuwa a saboda zazzabin cizon sauro.

Rahoton dai ya alakanta wannan matsalar ne da rashin tsabtar jiki da kuma ta muhallin da yara kan sami kan su a ciki.

Wanda kuma kashi 74 cikin dari na wannan matsalar na faruwa ne a Nahiyar Afirka da kuma Kudu maso gabashin nahiyar Asiya.

Tsabtar jikin yaro da ta muhallin da yaron yake abu ne da ke tafiya kafada da kafada.

Muna dauke da rahotanni daban-daban kan batun tsaftar yaran da kuma muhallinsu a shirin Haifi Ki Yaye da BBC Hausa na wannan makon.