Kura ta fara lafawa a garin Jos

Kura ta fara lafawa a garin Jos
Image caption Garin Jos ya dade yana fama da rikicin addini da na siyasa

Rahotanni daga jihar Filato a Najeriya na cewa kura ta lafa bayan tashin hankalin da aka fuskanta ranar Alhamis a Jos, inda a kalla mutane 40 suka hallaka.

An dai an zargi jami'an tsaro da kashe fararen hula da dama amma kuma hukumomin tsaron cewa suke yi farar hular ne suka fara bude wuta ga sojoji. Kimanin shekaru goma kenan jihar ta Filato na yawan fuskantar tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini inda dubban mutane suka rasa rayukansu.

Masana na ganin matsalar ta jihar Filato na daya daga cikin manyan kalubalen tsaro dake gaban Najeriya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai jami'an tsaro da dama a birnin na Jos da kewaye

Dattawan Arewa sun koka

Duka malaman addinin Musulunci da na Kirista sun yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa a garin na Jos, amma kuma mabiya addinan biyu na ci gaba da zargin juna kan lamarin.

Ita ma Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, ACF, ta nuna damuwarta kan tashin hankalin na baya-bayan nan a jihar ta Filato.

"Tashe-tashen hankula a jahar Filato na bakanta mana rai matuka domin babu dalilin afkuwar su ba," a cewar sanarwar da ta aikewa manema labarai a Kaduna.

Ta kuma yi kira ga Musulmi da Kirista da su bi tafarkin yafewa juna, maimakon na ramuwar gayya.

Har ila yau kungiyar ta ce atata fahimtar, rikicin ba shi da alaka da addini ko kadan.