Ra'ayi; Menene darasi kan rikicin Libya?

Taro kan kasar Libya
Image caption Taro kan kasar Libya.

Tun a cikin watan Fabrairu ne guguwar sauyin dake kadawa a wasu kasashen Larabawa, ta shiga kasar Libya, kuma daga lokacin ne ake ta artabu tsakanin dakarun 'yan tawayen da kasashen kungiyar NATO ke mara wa baya, da kuma dakarun Kanar Gaddafi.

Yanzu haka, 'yan tawayen na Libya sun kame galibin birnin Tripoli da sauran sassan kasar, amma har yanzu akwai yankuna da dama, inda sojojin da ke biyaya ga Kanar Gaddafi su ka ja daga.

Daya daga cikin irin wadannan yankuna, shi ne birnin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafin.

Duk da cewa har yanzu Kungiyar Tarayyar Afrika ba ta amince da gwamnatin 'yan tawaye ba, to amma kasashen Afrika da dama, ciki har da Najeria da kuma Nijar, sun fito sun nuna goyon bayansu ga 'yan tawayen.

Tambayar da ake yi yanzu haka ita ce: Wane irin tasiri ne wannan sauyin da ake samu a kasar ta Libyar zai yi a wannan yanki, da ma Afrika baki daya?

To domin tattaunawa kan abubuwan dake faruwa a Libyar, ba ya ga masu saurarenmu dake kan layi, mun kuma gayyaci baki da suka hada da:

.... Ambasada Isuhu Bashar, tsohon jakadan Nijar a Libiya; da kuma Sherrif Muhammad Zaydan Waddani, wakilin 'yan tawayen Libyar a Nijar, wadanda dukansu ke birnin Yamai; .... Akwai kuma

Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Nijeriya a Sudan, kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum;

.... Sai kuma a Accra Ghana, muna tare da Sheikh Usman Bari, tsohon jami'in jakadancin kasar ta Ghana, kuma masanin tarihi.