Turkiyya ta kori jakadan Isra'ila

Flotilla Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A bara ne sojojin Isra'ila suka kaddamar da hari kan jirgin

Turkiyya ta kori jakadan Isra'ila a kasarta tare da soke duk wata huldar soji tsakaninta da Isra'ilar domin martani kan sakamakon binciken harin da sojin Isra'ila suka kai kan jirgin ruwan flotila.

Sakamakon rahoton na Majalisar Dinkin Duniya da aka tsaigunta ya gano cewar, Isra'ila bisa ka'ida na da 'yancin katse hanzarin jiragen ruwan, amma kuma ya soki lamirin irin karfin da dakarun nata suka yi amfani da shi.

Turkawa tara ne aka kashe a lokacin harin da sojin kundumbala na Isra'ila suka kai bara kan masu fafutukar kare 'yancin Palasdinawa, wadanda suka yi yunkurin karya killacewar da Isra'ila ta yiwa yankin Gaza.

Ministan harkokin wajen Turkiyya, Ahmet Davu-toglu, ya umarci Jakadan Israila, da ya fice daga cikin kasar nan zuwa tsakiyar makon gobe, sannan ya ce "kowace kasa za ta kuma janye sauran manya manyan Jami'an diplomasiyyarta zuwa gida".

Dama dai an taka burki akan duk wasu harkokin dangantaka tsakanin Turkiyya da Israila, bayan rikicin da ya biyo bayan mamayen da Israila ta yiwa wasu jiragen ruwa dake dauke da kayan agaji.

An dade ana tattaunawa

Ministan ya kuma ce za'a dakatar da duk wata yarjeniya ta fuskar soji da ke tsakanin Turkiyya da Israila.

"Gwamnatinmu za ta bayar da goyan bayan ga duk wani yunkuri na gurfanar da Isra'ila a gaban kuliya da mutanen dake cikin jirgin ruwan za su yi".

Jami'ai daga kasashen biyu, sun shafe wata da watanni suna kokarin sasantawa a tsakaninsu akan al'amarin da ya faru.

Sau ukku ana jinkirta fito da rahoton na Majalisar Dinkin Duniya domin bayar da damar yin haka.

Sai dai a karshe Isra'ila ta ki amincewa da bukatar da Turkiyya ta nema ta cewar akalla ma dai ta nemi ahuwa akan al'amarin.