An kashe mutane a garin Biu, jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno dake Arewacin Najeriya na cewar mutane akalla tara ne suka rasu, yayinda wasu karin hudu suka jikkata, aka kuma kona shaguna da dama, a wani rikici da ya barke bayan da wasu jami'an soji suka kai samame tare da yin harbin kan mai uwa- da- wabi a cikin garin Biu.

Daga cikin wadanda suka ji raunin har da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Bornon.

Jami'an sojan sun kai samamen ne, sakamakon kisan da aka ce wasu 'yan bindiga sun yi wa wani jami'in soja a kauyen Borgu dake kusa da garin na Biu a daren jiya.

Rundunar Hadin Gwiwar Samar da Tsaro a jihar Bornon, JTF ta tabbatar da abkuwar lamarin; sai dai ta ce ba za ta iya yin cikakken bayani ba, tana mai cewa lamarin na karkashin Rundunar Soji ta 23 ne dake jihar Adamawa.