Martani kan kafa dokar ta-baci a Jos.

Gwamnatin jihar Pilato a Nijeriya ta ce kafa dokar ta-baci a jihar ab shi zai kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi ba.

Hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan yada labari an jihar, Mr Yiljap Abraham, sa'ilin da yake maida martani kan kiraye kirayen da wasu ke yi cewa, hukumomin jihar Pilaton sun gaza wajen samar da tsaro.

Mr Abraham ya ce maimakon irin wannan kira , kamata yayi a taya su da addu'a, domin samun zaman lafiya.

Jihar ta Pilato dai na fuskantar rikicin kabilanci da addini, inda ko a shekaranjiya, sai da aka kashe mutane akalla arba'in, a wani tashin hankali tsakanin musulmi da Kirista.