Obama ya yi amai-ya-lashe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi watsi da matakan tsaurara dokokin gurbata muhalli a kasar wadanda a baya suke cikin manyan manufofin gwamnatinsa.

A yanzu Mista Obama ya umurci hukumar kare muhalli ta kasar da ta dakatar da shirinta na rage yawan hayakin da ake fitarwa.

Matakin dai ya zo ne biyo bayan alkaluman da suka nuna cewa ba a samu ci gaba ba wajen samarwa 'yan kasar ayyukan yi a watan jiya.

Hakan dai ya nuna yadda shugaban kasar ya kadu dangane da yadda tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal.

'Yan kasuwa dai sun yi marhabin da matakin, sai dai masu kare muhalli sun zargi Shugaba Obama da bayar da kai bori ya hau ga masu gurbata muhalli.