Bukatar sanya dokar ta-baci a Filato

Image caption Jonah Jang

Wadansu daga cikin 'yan majalisar Dattawa a Najeriya sun ce za su gabatar da kudirin dokar da zai sanyawa jihar Filato dokar ta-baci.

Daya daga cikinsu, Sanata Kabiru Gaya, ya ce rikicin jihar ya munana kuma gwamnatin jihar ta gaza shawo kansa, don haka ne 'yan majalisar za su bukaci magance rikicin.

Ya kara da cewa idan gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da bukatarsu, za su tursasa mata yin hakan.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da rikice-rikice inda ko da a baya-bayan sai da mutane da dama suka rasa rayukansu sakamakon wani rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci.