Takunkumin kasashen Turai a kan Syria

Masu zanga zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga a Syria

Tarayyar Turai ta bada sanarwar kampanoni da mutane a kasar Syria wadanda aka haramtawa kasashen tarayyar turan yin huldar kasuwanci da su. Kampanonin sun hada da wani banki mallakar gwamnati, da wani kampanin sufuri, da kuma wani kampanin saka-jari.

Matakin da tarayyar turan ta dauka na baya baya ya biyo bayan shawarar da aka zartar ne a jiya Juma'a, cewar kasashen tarayyar Turan su daina sayen mai daga Syria.

'Yan adawa sun ce an kashe mutane akalla goma sha uku, a jerin zanga zangar nuna kyamar gwamnati na baya baya, bayan kammala sallar Juma'a a jiya.