An kashe mutane akalla talatin a Somalia

Akalla mutane 30 sun hallaka, wasu karin dari daya kuma suka samu raunuka, a sakamakon wani mummunan fada da aka yi a wani gari dake tsakiyar Somaliya.

An kai wadanda suka ji raunikan wani asibiti da kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontrieres ke daukan nauyin gudanarwa a garin Galkayou, wanda rabinsa ke cikin yankin Puntland, daya rabin kuma cikin yankin Galmudug.

Hukumomin yankin na Puntland sun ce daya daga cikin kwamandojin sojan su, ya hallaka a fadan.

Rikicin dai ya hada kabilu biyu ne, amma mahukuntan Puntland sun ce an yi fadan ne tsakanin sojojin yankin da wata kungiya mai alaka da mayakan al Shabaab.