Ana yi wa garin Bani Walid na Libya kawanya

Dakarun 'yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zura ido don ganin ko dakarun Bani Walid za su mika wuya.

Dakarun 'yan tawaye a Libya sun kusa cimma garin Bani Walid, wanda ke daya daga cikin yankunan da ke hannun dakarun da ke biyaya ga Kanar Gaddafi.

Tun farko dai 'yan tawayen sun ba sojin na Gaddafi wa'adin su mika wuya ko kuma su fuskanci hari.

Daruruwan 'yan tawaye ne dai cikin manyan motoci dauke da manyan makamai suke dannaaw zuwa garin daga sassa uku na kewayen garin, wanda ke kudu maso gabashin Turabulus, babban birnin kasar.

Moftah Mohammed yana cikinsu. Ya kuma sheda wa BBC cewa, ‘Yanzu muna kan iyakar Bani Walid, tsakanin Tarhouna da Bani Walid.

‘Muna hada kai da 'yan tawayen dake Misrata. Insha Allah muna sa ran shiga garin yau ko gobe.’

An dai yi imanin cewa wasu daga cikin iyalan Kanar Gaddafi sun bi ta Bani Walid ne wajen tserewa daga Turabulus, kuma kwai rahotanni da ke cewa wasu daga cikinsu har yanzu suna garin na Bani Walid.