Ministan tsaron Cuba ya mutu

Image caption Taswirar kasar Cuba

Gidan talbijin na kasar Cuba ya sanar da mutuwar Ministan tsaron kasar, Julio Casas Regueiro, wanda ya shahara a lokacin juyin juya halin da aka gudanar a kasar a shekarun baya.

An bayyana cewa Janaral Casas Regueiro, dan shekaru saba'in da biyar, ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Shi ne mutumin da ke lura da batutuwan da suka shafi kudade na rundunar sojin kasar har zuwa shekarar 2008 inda shugaba Raul Castro ya nada shi a mukamin ministan tsaro.

Shi dai Julio Casas Regueiro, tsohon Akanta ne wanda kuma ya yi yaki da Fulgencio Batista, mutumin da Fidel Castro ya hambarar da gwamnatinsa a watan Janairun 1959.