An kara kashe mutane a jihar Filato

Image caption Gwamnan Filato, Jonah Jang

Rahotanni daga Jihar Filato na cewa wasu mutane takwas 'yan gida daya sun rasa rayukansu a wani farmaki a yankin Heipnag da ke karamar hukumar Barikin Ladi jiya da dare.

Lamarin dai ya faru ne kimanin sa'o'i ashirin da hudu bayan da wasu matasa a garin na Heipang suka far ma wata mota mai dauke da mutane bakwai da ta tashi daga Mangu zuwa birnin Jos, inda kawo yanzu ba a ji duriyar mutane uku ba, hudun kuma suka sha dakyar.

Sai dai direban motar ya ce ya ga an tura fasinjojin nasa a gefen titi and kokarin kashe su

Hakan ya biyo bayan wasu kashe-kashen ne da aka yi a jihar.

An kwashe tsawon wannan makon ana ta fama da kashe-kashe a jihar ta Filato, kashe-kashen da ta dade tana fama da su da ke da nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa.