An gudanar da zanga-zanga a Israela

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Masu zanga-zanga a Israela

Kimanin mutane dubu dari hudu ne suka gudanar da zanga-zanga a Israela domin nuna rashin jin dadinsu game da tsadar rayuwa a kasar.

An dai gudanar da babban gangami ne a birnin Tel Aviv, inda anan ne aka fara zanga-zangar a farkon wannan shekarar.

Masu gudanar da zanga-zangar sun fito ne daga bangarori da dama na al'ummar kasar, inda suka bukaci gwamnati ta rage kudin gidaje, da rage haraji, tare da inganta bangaren ilimi a kasar.

Kazalika masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta rika rabon arzikin kasar dai-dai-wa-dai-da.