Chirac zai bayyana a gaban kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jacque Chirac

A yau Litinin ne tsohon shugaban Faransa, Jacques Chirac, zai bayyana a gaban kotu don amsa tuhumar da ake yi masa ta daukar dawainiyar jam'iyarsa ba bisa ka'ida ba.

Ya dauki dawainiyar jam'iyar ne a lokacin da ya ke rike da mukamin magajin garin Paris.

Wannan ne dai karon farko da wani tsohon shugaban kasar ke fuskantar shari'a tun bayan da aka yankewa tsohon shugaban kasar, Marshall Petain, hukuncin cin amanar kasa bayan yakin duniya na biyu.

Ana nuna shakku akan ko Mista Chirac zai bayyana a gaban kotun da kansa bayan da lauyoyinsa suka nuna shaidun da ke cewa yana fama da cutar gushewar tunani.

Sai dai wadansu 'yan kasar sun ce lafiyarsa lau don haka dole ya fuskanci shari'a.