Hukumar EFCC na yin wani taro kan cin hanci da ta'addanci a Najeriya

An fara wani taro a Najeriya don nemo hanyoyin yaki da masu tallafa wa ta'addanci da kuma ayyukan da ke dakushe tattalin arzikin kasa.

Hukumar yaki da masu y wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ce ta shirya taron, inda aka gayyato kwararru don horar da jami'anta ta wannan fuska.

Najeriyar dai na daga cikin kasashen duniya da ke fama da matsalar cin hanci da rashawa, wadda kuma a baya-bayan nan take fuskantar hare-haren da ake danganta wa da ta'addanci.