Bincike kan alakar Burtaniya da gwamnatin Gaddafi

David Cameron Hakkin mallakar hoto PA
Image caption David Cameron, Pirayim Ministan Birtaniya

A binciken da ake gudanarwa a kan ko Birtaniya nada hannu a azabtar da wadanda ake zargi da ta'adadanci, yanzu za a dubi sabbin zarge-zargen cewa akwai alaka ta kut-da-kut tsakanin Birtaniya da gwamnatin Gaddafi.

Binciken ya ce zai nazarci wasu takardun da aka gano kwanannan a Tripoli.

Takardun sunce Birtaniya ta taimaka wajen kai wani, da aka zarga da aikata ta'addanci zuwa Libya don yi masa tambayoyi.

Mutumin dai yanzu kwamanda ne a bangaren 'yan tawayen Libya kuma ya ce, an azabtarda shi.

Sai dai tsohon sakataren wajen Birtaniya Jack Straw ya ce, bai san da maganar ba.