Mukarraban Kanar Gaddafi suna Nijar

Taswirar Jumhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jumhuriyar Nijar

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce, shugaban tabbatar da tsaro a kasar Libya, a karkashin Kanar Gaddafi, ya isa birnin Yamai.

Rahotannin sun ce, Mansur Daw ya shiga Nijar din ne, tare da wasu tsoffin jami'an gwamnatin Gaddafi su kimanin goma, wadanda suka hada da Janar Ali Kanan da kuma Husseini al Kouni, tsohon jakadan Libya a Nijar din a farkon shekarun 2000.

Tawagar dai ta isa Nijar din ne tare da rakiyar tsohon shugaban kungiyar 'yan tawaye ta MNJ, Aghali Alambo.

Gwamnatin Niger ta amince da Gwamnatin 'yan tawayen Libyar mako guda da ya wuce.

Har yanzu dai ba a san inda Gaddafi yake ba.