Jami'an Red Cross za su ziyarci fursunoni a Syria

Wasu mata masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mata masu zanga-zanga a Syria

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce a karon farko, gwamnatin Syria ta baiwa tawagar ta iznin ziyartar fursunonin kasar.

Shugaban kungiyar Red Cross din, Jakob Kellenberger ya ce ma'aikatan kungiyar sun ziyarci wadanda ake tsare da su a babban gidan yarin kasar dake Damascus a jiya lahadi.

Da yake magana bayan wata ganawa da shugaba Bashar al- Assad, Mista Kellenberger ya ce yana fata za'a ba su iznin ziyartar sauran wadanda ake tsare da su.

Wani kakakin kungiyar Red Cross a Geneva, Hicham Hassan ya ce ziyayar za ta bude kafar taimakawa wadanda ake tsare da su a kasar ta Syria..

Ya ce kungiyar agaji ta Red Cross na aiki da tare da kungiyar agajin Red Crescent ta Syria don biyan bukatun agajin da kan taso a wuraren da ake fama da tashin hankalin.