NATO zata daina ba Afghanistan fursunoni

Rundunar ISAF, a Afghanistan
Image caption Rundunar ISAF a Afghanistan

Rundunar tsaron kasashen duniya, karkashin jagorancin kungiyar NATO dake Afghanistan, ISAF ta dakatar da tura mutanen da take tsare da su zuwa gidajen kurkukun kasar, sakamakon zargin da aka yi na cewa ana azabtar da su a can. Azabtarwar ta hada da duka, da mesar roba, da kuma cinna ma su wutar lantarki.

BBC ta samu labarin cewa matakin dakatarwar ya shafi larduna takwas ne da kuma Cibiyar yaki da ta'addanci ta kasar.

Wakilin BBC ya ce da dama daga cikin zarge-zargen na kunshe a cikin wani rahoton da ba a wallafa na Majalisar Dinkin duniya.