An ce kiwon lafiya na kara muni a Afrika

Wani rahoto na kungiyar agaji ta Save The Children da aka wallafa yau, ya nuna cewa, yiwuwar kananan yara su rasu, a kasashen da ake da karancin ma'aikatan kiwon lafiya ya ninka sau biyar idan aka kwatanta da inda ake da matakan kiwon lafiyar ingantattu.

Kasasahen Switzerland, da Finland na daga cikin inda rahoton ya ce ana da matakan kiwon lafiya da suka fi inganci a duniya.

Kasashen Nijeriya da Niger kuma na daga cikin kasashe ashirin da babu ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

Kasar Chadi ce ta karshe, Somalia na bi ma ta, yayinda Nijeriyar take ta biyar daga kasa.