Hukumar leken asirin Najeriya ta gano wurin hada bam

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Hukumar leken asiri ta SSS a Najeriya, ta ce ta gano wani waje da ake hada bam a garin Suleja dake kusa da birnin Abuja.

Haka kuma hukumar ta ce ta kama mutane shidda dake da alaka da kungiyar nan ta Jama'atul Ahlul Sunna lil da'awati wal jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram.

Kakakin hukumar, Merlyn Ogah, ta ce a wannan wuri sun kuma gano abubuwan da ake hada bam, wadanda aka shirya da niyyar kai hari.

Kungiyar ta Boko Haram dai ta yi ikirarin kai hare-hare a sassan Najeriyar.

Na baya-bayan nan shi ne harin da ta ce ta kai kan ofishin majalisar dinikin duniya dake Abuja.