Yawan biloniyoyi sun haura 270 a China

Wani sabon jadawali na jerin sunayen hamshakan masu kudi a China ya nuna cewa yawan wadanda suka mallaki sama dala miliyan dubu ya kai mutane sama da dari biyu da saba'in.

Ana danganta bunkasar wannan budi da mutane ke samu ne da kasuwanci, da harkar gine-gine da ke ci, da kuma nasarar da aka samu wajen sa ido akan kasuwar hada-hadar hannayen jari.

Mutum mafi kudi a Chinar din dai yanzu shi ne Liang Wengen, wanda yake harkar kayan gini.

An kiyasta cewa ya mallaki dala biliyan goma sha daya.