Akalla mutane tara suka hallaka a Delhi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani da yaji ciwo a harin na Delhi

Wani babban jami'i a gwamnatin India ya ce mutane akala tare ne suka hallaka yayinda arbain da biyar sun samu raunuka a fashewar wani bam a wajen wata babbar kotu dake Delhi babban birnin kasar.

'Yansanda sun ce fashewar bam din ya faru ne da misalin karfe goma na safiyar yau a lokacin da jama'a suka taru a wurin.

A watan Mayun daya gabata an samu fashewar wani bam a wajen kotun abun da ya janyo rudani duk da cewa babu wani wanda ya jikkata.

Harin yau shine na farko a India tun bayan jerin bama bamai guda uku da aka kaiwa wasu anguwanin Mumbai a watan yuli da ya yi sanadiyar mutuwar mutane ashirin.

An rika zargin kungiyar Indian Mujahedeen da kai hare haren.