Gaddafi ya musanta cewa ya tsere zuwa Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daya dag cikin jerin gwanon motocin Libya

Kanar Gaddafi yayi fatali da abinda ya kira karairayi da kuma neman juya tunanin mutane ta hanyar yada jita jitar cewa ya tsere zuwa Niger.

Yayi wannan jawabi ne ta wayar taraho da gidan talabijin na kasar Syria wanda ya ce, kiran ya zo ne daga cikin Libya.

Kanar Gaddafi ya kuma yi alkawarin cewa, dakarunsa za su yi nasara kan kungiyar NATO da gwamnatin rikon kwaryar yan tawayen.

Wannan ne dai sakonsa na farko cikin kwanakin baya bayan nan.

Rahotanni dai na nuna cewa, cikin kwanakin da suka gabata, manyan jamian tsohuwar gwamnatin Kanar Gaddafi sun isa Niger, kuma akwai rade radin cewa Kanar Gaddafin zai bi su.