An ci gaba da shari'ar Hosni Mubarak

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zanga zanga da 'yan sanda na taho mu gama da juna

An koma bakin shari'ar da ake yiwa tsohon Shugaban Kasar Masar, Hosni Mubrak, a birnin Alkahira, inda ake fuskantar cacar baki matuka tsakanin lauyoyi masu gabatar da kara da kuma wadanda suke kare shi.

Al'amarin har ya kai ga wasu lauyoyin ficewa daga cikin zauren shari'ar suna masu cewar yamutsin ya yi yawa.

To sai dai duk da haka, tun da sanyi safiya masu zanga-zanga suka fara hallara a kofar ginin kotun suna dauke da kwalaye da kyallaye.

"Inda suke cewa Bamu gaji ba, -- domin babu wani zabi ga wannan juyin juya hali".

Dama dai a zaman da aka yi na ranmar Litinin, sai da aka kai ga baiwa hammata iska a tsakanin lauyoyin.

An kuma yi taho-mugama tsakanin magoya baya da kuma masu adawa da tsohon shugaban na Masar.

Masu shigar da kara sun kira wasu manyan jami'an yansanda su hudu wadanda ake ganin za su gabatar da shaida akan irin rawar da Mr Mubarak ya taka wurin murkushe masu zanga zanga.

Sai dai a cewar daya daga cikin lauyoyin, mutumin daya fara gabatar da shaida ya ce shi be san da umurni a harbi masu zanga zangar ba .