An kaiwa ofishin jakadancin Niger hari a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar

A jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun tabbatar da harin da aka kai ma ofishin jakadancinta a Tripoli babban birnin kasar Libya,sai dai sun ce ya zuwa yanzu ba su tantance ko su wane ne suka kai harin ba.

Al'amarin ya faru dai a daidai lokacin da gwamnatin ta nijar ta bayar da tabbacin kasancewar wasu manyan jami'an gwamnatin Ghadafi a wajenta,wadanda tuni suka samu mafaka a kasar ta Nijar.

Harin a cewar wadanda suka gani da idanunsu a birnin Tripoli yayi ma ofishin jakadancin Nijar kaca kaca.

Sai dai hukumomin Nijar din sun ce zasu gudanar da bincike akan batun.