Taro kan fari a Kusurwar Afrika

Image caption Matsalar fari a Somalia

'Yan siyasar a Gabacin Afrika da kuma kungiyoyin ayyukan agaji suna yin taro a kasar Kenya don nemo hanyoyin da ya kamata a tunkarar farin da ke fuskantar yankin.

Farin dai ya shafi mutanen da suka kai milyan goma sha biyu.

A kasar Somalia inda farin ya fi kamari, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane kamar kashi ukku na milyan guda ne ke fuskantar halaka sanadin yunwar cikin 'yan watannin da ke tafe.

"Ina ganin saurin yankin ya ware kudi masu yawa don aikin gona, watakila dalili ke nan sauran yankin bai shiga cikin wahala ba kwarai," a cewar Luka Alivoni na Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

Mr Luka ya kuma ce yunwa ta fi kamari a Somalia ne saboda rashin ware kudi don inganta aikin gona.

Masu shirya taron sun ce ba na neman taimako ba ne, illa dai dama ce ta samo hanyoyin dogon lokaci na magance matsalar farin.