" Kashe Baha Moussa, abun assha ne" In ji Cameron

David Cameron Hakkin mallakar hoto BBC News 24
Image caption David Cameron

Pira ministan Biritaniya, David Cameron, ya bayyana kashe wani dan Iraqi farar hula da ke hannun sojin Biritaniya a matsayin wani al'ammari mai tayar da hankali matuka, kuma na assha.

Ya ce lalle ne sojin Biritaniyar su tabbata cewa irin wannan lamari bai sake aukuwa ba.

Mr Cameron yana jawabi ne a kan sakamakon binciken da ya nuna cewa sojin Biritaniya ne suka yi ta dukan Baha Mousa har sai da ya mutu, bayan da suka yi ma shi raunika har tasi'in da ukku a shekara ta 2003 a birnin Basra na Iraki.

Phil Shine, lauyan da ya jagoranci lauyoyin da ke wakiltar wadanda abin ya shafa, ya ce ba wannan ta'asar ce kawai ta auku ba, akwai wasu da dama.