Kwalara na bazuwa a wasu jihohin Arewacin Najeriya

Wasu likitoci a Najeriya
Image caption Wasu likitoci a Najeriya

A Najeriya cutar amai da gudawa ko Kwalara na bazuwa a wasu sassan jihohin arewacin kasar a cikin yan kwanakin nan.

A baya bayan nan dai ma'aikatar lafiya ta kasar ta yi gargadin bazuwar cutar a fadin kasar bayan da ta fidda alkaluma cewa a wasu jihohin arewacin kasar goma sha daya, cutar ta hallaka mutane kusan dari hudu kuma ta kama kusan dubu bakwai.

Daya daga cikin abubuwan da ke haddasa cuitar ta Kwalara dai, shi ne cin gurbataccen abinci ko ruwan sha maras tsafta.

Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da aka samu bullar cutar , kuma har ta hallaka mutane da dama ya zuwa yanzu.