'Yan kwadago sun bijirewa jami'an tsaro

Taswirar Najeriya
Image caption An dade ana sa'insa kan batun sabon albashin

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta gudanar da wani gangami a jihar Enugu duk da kokarin da ake zargin gwamnatin jihar ta yi na hana gudanar da shi.

Kungiyar kwadagon ta je jihar ta Enugu ne domin nuna adawa da matakin gwamnatin jihar na kin biyan sabon tsarin albashin da aka amince da shi a kasa baki daya.

"Sojoji da 'yansanda dauke da manyan bindigogi sun tsare bakin otel din da muke zaune, suna hana mutane isowa garemu," a cewar shugaban kungiyar Abdulwaheed Umar.

"Gwamnatin Enugu ce ta shirya wannan makarkashiyar, kuma hakan ba zai hana mu ci gaba da fafutukarmu ba," kamar yadda Abdulwaheed ya shaida wa BBC.

Sai dai yayin da wakilin BBC ya tuntubi daraktan yada labarai na gwamnan jihar Enugu, Mista Chukwudi Achife, game da zargin da kungiyar kwadagon ta yi, ya ce gwamnatinsu ba ta da hannu a batun tsare shugabannin kwadagon. Sai dai a tuntubi 'yan sanda.

Amma kuma wakilin namu ya buga wayar jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Enugun, Mista Ebere Amarizu tana ta kadawa bai dauka ba.