An sabunta: 9 ga Satumba, 2011 - An wallafa a 12:43 GMT

Kididdigar asarar da aka yi a harin 9/11

 • Kididdiga: Asarar da aka yi a harin 9/11

  Kalubalen harin 9/11 da aka kai a Amurka batu ne da ya shafi duk duniya, lamarin da ya janyo yakin da ya salwantar da rayukan fiye da mutane 250, 000 a cikin shekaru goma. Latsa wannan shafin na BBC (Hausa) domin sanin adadin abinda harin 9/11 ya janyo.

 • Sojan Amurka na farko da aka kashe

  Evander Earl Andrews shi ne Sojan Amurka na farko da ya rasu a matakin da soji suka dauka biyo bayan harin 9/11. Ya rasu a wani hatsari a sansanin soji da ke Qatar, a kokarin marawa kutsen da aka yiwa Afghanistan baya.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Fararen hular da aka kashe a Iraqi

  Tun bayan fara yakin da Amurka ta jagoranta, akalla fararen hula 125, 000 ne suka rasu. Ana kuma tunanin kamar an rage yawan adadin ne. Har yanzu yakin bai kare ba: fararen hula masu yawa na ci gaba da mutuwa.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Rayuwar Musulmi a Amurka tun shekarar 2001

  Yayin da mafi yawan Musulman Amurka ke cewa suna kara shan wahala kasancewarsu Musulmai a kasar, bayan harin 9/11, kashi 48 cikin dari da kuma kashi 32 cikin dari a cikinsu na cewa al

  Madogara: Cibiyar bincike ta Pew, 2011

 • Karin wadanda ke neman aiki da CIA

  A cikin kowanne mutane biyu da ke neman aiki da hukumar leken asiri ta CIA a shekarar 2001, shekara guda bayan nan an samu mutane uku da ke yunkurin shiga.

  Madogara: Mujallar New York, 2002

 • Yan Iraqin da suka rasa muhallinsu

  Kimanin 'yan Iraqi miliyan 3.5 ne (wato mutum daya cikin kowanne goma) kawo yanzu suka rasa muhallinsu. Wadansu miliyoyin al'ummar Iraqin kuma sun tsere daga kasar.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Lokacin da tagwayen hasumiyoyin WTC suka dauka kafin su fadi

  Lokacin da tagwayen hasumiyoyin suka dauka suna ci da wuta: Hasumayar kudu: Dakikokiu 56; Hasumiyar Arewa: Dakikoki 102: Lokacin da suka dauka kafinn su fadi: Dakikoki 12

  Madogara: Mujallar New York, 2002

 • Yan jaridar da suka mutu

  255

  Adadin 'yan jaridar da suka rasu a yake- yaken Iraqi da Afghanistan da kuma Pakistan.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Yaran Iraqi

  A shekarar 2010, an kiyasta cewa kashi 28 cikin dari na yaran Iraqi sun sha wahala saboda matsalolin da suka danganci tashin hankali, kuma sannu a hankali adadin na karuwa.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Kudaden da Amurka ta kashe a yaki bayan harin 9/11

  Kiyasi na nuni da cewa Amurka ta kashe tsakanin dala triliyan 3.2 zuwa dala triliyan 4 a yake- yaken da ta yi a Iraqi da Afghanistan da kuma Pakistan

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Yan Afghanistan din da suka rasu

  Adadin wadanda suka rasu a duk shekara na karuwa tun daga lokacin da aka fara yakin a watan Oktobar shekarar 2001. Mutanen da suka rasu a saboda yakin sun zarta wadanda suka rasu a lokacin da kungiyar Taliban ke rike da iko.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Adadin wakokin da ake gani basu dace a saurara ba, bayan harin 9/11

  Kungiyar Clear Channel Communication wadda ke aiki da gidajen radiyon Amurka fiye da 1,170 ta fitar da jerin wakoki 165 da gidajen radiyon za su dakatar da sakawa na dan wani takaitaccen lokaci, cikinsu harda wakar "Highway to Hell" ta AC/DC

  Madogara: Clear Channel Communication, Wikipedia

 • Yan Pakistan din da suka rasu

  Tun shekarar 2004, yawan fararen hular da suka rasu saboda fadace-fadace a Pakistan, sun zar ta wadanda suka rasu a Afghanistan. Harin da jiragen Amurka da basa dauke da mutane ke kaiwa ya kashe akalla mutane 2000, wadansu daga ciki fararen hula.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Diyyar da aka baiwa 'yan mazan jiyan Amurka

  Fiye da mutane 555, 000 ne Ma'aikatar kula da harkokin 'yan mazan jiyan Amurka ta yiwa rajista da suka gamu da nakasa, daga lokacin zuwa karshen shekarar 2010.

  Madogara: Cibiyar Watson, Jami'ar Brown, 2011

 • Adadin sojin kawance da aka rasa a Iraqi da Afghanistan

  A farkon watan Satumbar 2011, kiyasin adadin dakarun hadin gwiwar da suka rasa rayukansu a Iraqi sun kai 4792, idan aka kwatanta da 2693 da aka yi a Afghanistan.

  Madogara: Cibiyar kidayar wadanda hatsari ya rutsa dasu a Iraqi, 2011

 • Tarkacen da aka kwashe

  Rahotanni sun nuna cewa tarkacen da aka kwashe daga Cibiyar Kasuwanci ta Duniya a New York ya kai tan 1,506,124.

  Madogara: Mujallar New York, 2002

 • Inshorar da aka biya

  Kiyasin adadin Inshorar da aka biya a duk duniya game da harin ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 ya kai dalar Amurka biliyan 40.2

  Madogara: Mujallar New York, 2002

 • Adadin kudaden fansa da jami'an kwana-kwana da 'yan sandan birnin New York da ma ma tan da suka rasa mazajensu.

  Adadin kudaden da kowacce matar da mijinta ya rasu yayin aikin kashe gobara ta samu, da kuma matar dan sandan da ya rasu a harin 9/11, ko cikin shekara guda bayan harin: Dalar Amurka miliyan 1

  Madogara: Mujallar New York, 2002

 • Asarar da aka tafka a birnin New York

  Asarar da aka tafka a birnin New York sakamakon harin 9/11, ciki har da rashin aikin yi, da asarar haraji, da wadda ta shafi gine-gine, da gyara: Dalar Amurka biliyan 95.

  Madogara: Cibiyar Nazari akan harkar tsaron duniya, 2004

 • Harajin sararin samaniya da Amurka ta yi asara

  Adadin da Amurka ta yi asara a harajin sararin samaniya sakamakon rufe sararin samaniya saboda harin 9/11 ya kai dala biliyan 10.

  Madogara: Cibiyar Nazari akan harkar tsaron duniya, 2004

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.