Wani jirgin sama ya fadi a Angola

Hakkin mallakar hoto other

Wani jirgin sama na rundunar sojan Angola ya fado a lardin Huambo da ke tsakiyar kasar.

Mutane ashirin da shidda daga cikin talatin da biyun da ke cikin jirgin sun hallaka.

Daga cikin matattun har da Janar-Janar guda ukku.

Kawo yanzu ba a san musabbabin hadarin jirgin ba, wanda ya faru bayan tashin jirgin daga Huambon, akan hanyarsa ta zuwa Luanda, babban birnin kasar ta Angola.