An wallafa sunayen 'yan takara a Kamaru

Majalisar Hukumar shirya zabe a Kamaru ta wallafa sunayen 'yan takara 21 daga cikin fiye da 50, wadanda suka cancanci tsayawa a zaben shugaban kasa na ranar 9 ga watan Oktoba.

Shugaban Paul Biya wanda yake ci a yanzu haka yana daga cikin 'yan takaran.

Akwai kuma maata cikin 'yan takarar.

Samuel Fonkam Azu'u kakakin majalisar hukumar shirya zabe ya bayyana cewa kusan rasa cika sharadi guda ne ya sa aka soke yunkurin akasarin wasu da suka nuna sha'awar shiga takarar, wato rashin nuna shaidar biyan miliyan 5 na CFA.