Shugaban Man City Garry Cook ya ajiye aikinsa

Garry Cook
Image caption Mr Cook ya taka rawa wajen sauya fasalin Man City

Shugaban Manchester City Garry Cook ya ajiye aikinsa bayan da aka zarge shi da yin kalaman izgili kan cutar dajin da mahaifiyar Nedum Onuoha ke fama da ita.

Garry Cook ya mika takardar ajiye aikin ne bayan da bincike ya nuna cewa ya aike da sakon.

Wata sanarwa da kulob din ya fitar, ta tabbatar da cewa hukumomin kulob din sun amince da matakin na Mr Cook.

A yanzu haka kuma babban jagoran kulob din Khaldoon Al-Mubarak ya nemi ahuwa daga wurin Dr Onuoha kan abinda ya farun.

Mahaifiyar dan wasan wato Dr Onuoha, wacce kuma ita ce wakiliyarsa, ta taba aika wani sakon email a baya ga Marwood da Cook, tana cewa "cutar dajin" da ta ke fama da ita, ba za ta hanata ci gaba da wakiltar dan nata ba.

Daga nan ne ta samu wani sakon da ake zargin ya fito ne daga Cook inda ya yi kalaman izgili kan cutar tata.

Ya dai musanta aika wannan sako, yana mai cewa masu satar bayanai ne suka yi amfani da adreshinsa.

Karin bayani