Sasantawa tsakanin Isra'ila da Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters

Pira ministan Isra'ila ya ce har yanzu kasar na kan kudirin ta na mutunta 'yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Masar.

Ya ce gwamnatinsa na tattaunawa da Masar kan yadda za a samar da ingantaccen yanayin tsaron da zai ba da damar mayar da jakada da kuma sauran jami'an Diplomasiyyar Isra'ila gida, bayan da wasu masu zanga-zanga suka afkawa ofishin jakadancin Israi'la a birnin Alkahira.

Tun farko ministan yada labarai na Masar, Osama Haikal, ya zargi masu fafutikar da suka afka wa Ofishin jakadancin Israi'lar ranar juma'a da laifin zubar da kimar Masar a idanun duniya.