Shirin samar da ayukan yi na Obama

Hakkin mallakar hoto bbc

Shugaba Obama ya bada sanarwar bullo da wani shirin samar da aikinyi wanda zai ci kimanin dala billion dari da hudu da hamsin.

A cikin wata sanarwa da ba kasafai yake gabatarwa ba ga majalisar dokokin kasar, shugaba Obama ya ce, yana son tattalin arzikin Amurka ya farfado, bayan tsayawa cik din yayi.

Sai dai shugaba Obama yayi kira ga abokanen hammayasa da su zartar da kudurin domin taimakawa jama'ar kasar.

Shirin ya hada da rage kudin harajin da ake cirewa daga albashi, da sake samar da kudade ga cibiyoyin kudi masu bada rance sayen gidaje, da ceto ayukan malaman makarantu , tare da kara inganta makarantu zuwa na zamani da yin gyra akan hanyoyi da kuma samar da talafi ga marasa aikin yi har na wani tsawon lokaci.

Sai dai ana ganin kamar shugaban nada wata manufa wato ko 'yan jamiyar Republicans su amince da shirin ko ya gudanar da kamfe akan abun da zai nuna cewa masu hanu da shuni birnin washinton na farin cikin rage kudin harajin abokanensu masu arziki amma basa son yin haka ga marasa galihun kasar.