Ra'ayi Riga; Shekaru goma da Harin 9/11

Hari kan tagwayen bene a New York, Amurka
Image caption Hari kan tagwayen bene a New York, Amurka

Ranar Lahadi mai zuwa , idan Allah ya kaimu ne ake cika shekaru goma tun bayan hare-haren ta'addancin da aka kaiwa Amurka.

Dubban mutane ne, Amurkawa da sauran 'yan kasashen waje suka rasa rayukansu.

Nan da nan ne kuma Amurka ta dora alhakin hare-haren a kan kungiyar masu fafutukar Islama ta al Qaeda.

Da farko dai al-Qaedar, a karkashin jagorancin Osama bin Laden, ta musanta zargin, kafin daga baya ta dauki alhakin kai hare-haren, a shekara ta 2004.

Al-Qaeda ta ce ta yi hakan ne saboda irin goyon bayan da Amurka ke baiwa Isra'ila, da kuma kasancewar sojan Amurka a Saudiyya, tare da takunkumin da aka sa wa Iraki.

Hare-haren dai sun sa Amurka, tare da wasu kawayenta sun kaddamar da yaki a kan ta'addanci.

Sun mamaye Afghanistan inda suka kawar da gwamnatin Taliban, wadda suka zarga da bayar da mafaka ga 'yan kungiyar al Qaeda.

Daga cikin wadanda muka gayyato domin tattaunawa kan batun akwai;

Dokta Abubakar Dan Lami Alhassane, na jami'ar Bayero da ke Kano, wanda yana Amurka, lokacin da aka kai harin, sai Kwamishinan 'yan sandan jahar Rivers a Najeriya, Alhaji Sulaiman Abba, da Hon. Rabe Nasir, tsohon shugaban kwamitin yaki da ta'addanci a majalisar wakilan Najeriya, da Dokta Aliyu Tilde, mai sharhi kan al'amura a Najeriya, da Malam Musa Aliyu na cibiyar nazari kan yaki da samar da zaman lafiya ta Desmond Tutu, a birnin Liverpool, Ingila, da Injiniya Yusuf Abdulkarim Iyimoga a Kabul, babban birnin Afghanistan.