Sudan da kudancin Sudan zasu janye sojojinsu daga Abyei

Image caption Wani kauye a Abyei

Majalisar dinkin duniya ta ce, kasar Sudan da kuma sabuwar yantacciyar kasar Sudan ta Kudu, sun amince su janye sojojinsu daga iyakokin garin Abyei da ake takaddama akansa, nan da karshen wannan wata.

Mataimakin shugaban aikin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Edmond Mulet, ya ce an samu nasarar cimma wannan yarjejeniya ce saboda kasancewar dakarun Majalisar dinkin duniyar na sojojin kiyaye zaman lafiya daga kasar Habasha dake aiki a Abyei.

Gwamnatin Sudan da ta Sudan ta Arewa sun kasa cimma matsaya kan wanda zai mallaki garin, kuma takaddamarsu ta haddasa yaki a wurare da dama.

Wakilan bbc sunce kasashen biyu sun fara janye dakarunsu kuma hakan zai taimaka ainun wurin sassauta zaman zulumi a yankin.