Majalisar Dinkin Duniya ta koka kan rikicin Jos

Rikin Jos
Image caption Jos na fama da rikicin addini da na kabilanci

Majalisar dinkin duniya, ta bayyana damuwar ta kan sabbin rikice-rikicen da suka balle a wasu yankuna na jihar Pilaton Najerira tun farkon watan Agustan da ya gabata.

Majalisar ta ce dole ne a yi adalci wajen hukunta wadanda suke da hannu a tada zaune tsayen.

Ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da hakin bil adama wanda ke da mazauninsa a Geneva, ya ce ya damu kwarai da sabbin rikice-rikicen da suka barke a jihar to Pilato.

Rahotanni sun ce an yi sanadiyar kashe mutane akalla saba'in, daga karshen watan Agustan da ya gabata zuwa yanzu a jihar.

"Rikicin kabilanci da addini ya dabaibaye garin Jos da kewaye a tsawon shekarun da suka gabata," a cewar mai magana da yawun ofishin na Majalisar dinkin duniya mai kula da hakkin bil adama Rupert Colville a wani taron manema labarai.

Ya kara da cewa kowanne rikici na haifar da jerin hare-haren ramuwar gayya daga bangarori dabam-daban.

Ofishin na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi kira ga mahukuntan Najeriya da na jihar da abin ya shafa, da su dauki kwararan matakai na hana sake aukuwar rikice-rikicen, su kuma fara kokarin sasanta al'ummomin da rikicin ya shafa.

Rupert Colville ya kuma jaddada cewa: "Yana da muhimmanci a tabbatar da cewa an yi adalci, ta hanyar hukunta wadanda ake zargi da hannu a tashe-tashen hankulan, a kuma tallafa wa wadanda rikicin ya shafa da iyalansu".

Rikicin ya kazanta...

Wasu rahotanni daga jihar ta Pilato sun nuna cewa a ranar Alhamis da daddare wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen tsohuwar Foron.

BBC ta samu bayanan cewa akalla mutane 13 ne aka kashe a harin, wanda aka kai a karamar Hukumar Barikin Ladi.

Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da shafin wikileaks ya ce, manyan hukumomin tsaro na Najeriya sun ja kunnen gwamnan jihar Plateau, Jonah Jang, da kada ya gudanar da zabukan kananan hukumomin da ya haddasa tashin hankalin da aka yi a watan Nuwambar shekara ta 2008 a jihar.

Amma shafin na Wikileaks ya ce gwamna Jang yayi buris da wannan jan hankali da aka yi masa.

Zaben dai ya haddasa asarar rayuka da dama a jihar ta Plateau wadda har yanzu take fama da rikicin addini da kabilanci.

To sai dai kuma gwamnan jihar ta Filato, Jonah Jang, ya bayyana cewa bayanan na Wikileaks zancen kawai ne kuma baya nadamar gudanar da zabukan na 2008, inda a karamar hukumar Jos ta arewa aka bayyana cewa wani dan uwan gwamnan ne ya lashe zaben kana tashin hankali ya barke.