An gaano gawarwakin wasu 'yan Afrika a Libya

Wasu 'yan Afrika masu ci rani a Libya
Image caption Wasu 'yan Afrika masu ci rani a Libya

Jami'ai a Libya sun gano gawarwakin wasu mayaka kimanin 20 a cikin wasu ramuka 2 da aka gina a bakin hanya, kusa da Tripoli, babban birnin kasar.

Mazauna yankin sun ce galibin gawarwakin na 'yan Afrika bakaken fata ne da ake zargin sojan haya ne na Kanar Gaddafi.

Wakilin BBC ya ce ana jin an kashe mutanen ne kimain makonni 3 da suka wuce a lokacin fadan da aka yi na kwace iko da birnin Tripoli, kuma yanzu haka kwararrun masu binciken gawa da masu fafutukar kare Hakkin Bil Adama, na gudanar da bincike a kan ainihin abin da ya faru.

A halin da ake ciki kuma, dakarun 'yan tawayen Libyar sun cigaba da kai hari a kan garin Bani Walid, daya daga cikin garuruwan da suka rage a hannun magoya baya Kanar Gaddafi.