Al Sadr zai yi ban- iska ga Amurka

Malamin nan dan Shi'a mai kaifin ra'ayi, a Iraki, Moqtada al Sadr, wanda ke matukar adawa da Amurka, ya yi kira ga magoya bayansa da su dakatar da kai hare-hare a kan sojojin Amurka.

Moqtada al Sadr ya ce yana so ya baiwa sojojin na Amurka wata dama ta janyewa daga Iraki, nan da karshen wannan shekarar, kamar yadda aka cimma 'yarjejeniya da gwamnatin Irakin.

Ya ce idan sojojin na Amurka ba su janye ba, to za a cigaba da kai masu hare-hare masu munin gaske.

Yanzu haka dai, shugabannin siyasar Irakin na tattaunawa da Amurka kan yiwuwar kyale sojojinta su cigaba da zama a kasar ta Iraki, bayan wa'adin na karshen shekara.