Kazamin fada a garin Bani Walid

Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu adawa da Gaddafi ne ke da iko da yawancin Libya

An kashe dakarun da ke adawa da Gaddafi guda bakwai yayin da wasu 10 suka jikkata a kazamin fadan da ake gwabzawa na kokarin kwace iko da garin Bani Walid.

Dakarun sun ce mazauna garin ne suka yaudare su bayan da suka nuna musu cewa suna goyon bayansu.

Nato na ci gaba da kaiwa garuruwan da ke karkashin ikon Gaddafi hari, sai dai maharan ba su da karfin karbe garin, a cewar wakilin BBC.

A wani lamarin daban kuma, masu gadi 15 ne aka kashe lokacin da dakarun Gaddafi suka kai hari a matatar mai da ke garin Ras Lanuf.

Wani ma'aikacin mai da ya samu rauni ya ce wasu jerin gwanon motoci ne suka nufi matatar - wacce ke hannun Majalisar Rikon kwarya ta kasar - daga yankin mahaifar Kanal Gaddafi Sirte.

Matatar dai ba ta aiki a lokacin da aka kai harin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sa'ad shi ne na baya-baya a iyalan Gaddafi da ya fice daga kasar

Saadi Gaddafi ya samu mafaka

Harin ya zo ne kwana guda bayan da aka baiwa dan Kanal Gaddafi Saadi mafaka a jamhuriyar Nijar.

Ministan shari'a, kuma kakakin gwamnatin Nijar din, Malam Maru Amadou, shi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata hira da BBC a ranar Lahadi.

Ya ce jami'an tsaron Nijar ne suka gano Saadi Gaddafin, da wasu mutanen su takwas, kuma yanzu haka suna yankin Agades, a kan hanyarsu ta zuwa Yamai, babban birnin kasar.

A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, mukarraban Kanar Gaddafi da dama sun shiga jamhuriyar ta Nijar.

A yanzu masu adawa da Gaddafi na iko da mafi yawancin Libya cikin harda Tripoli babban birnni kasar. Yayin da magoya bayansa ke rike da garuruwa uku da suka hada Bani Walid da Sirte.

Har yanzu ba a san inda Kanal Gaddafi ya ke ba. Ya dai bayyana cewa a Libya zai mutu.

Jama'a dai a yanzu sun fara ficewa daga garin na Bani Walid.