Birtaniya zata yi gyara ga aikin banki

Gwamnatin Birtania ta ce zata ci gaba da kaddamar da manyan sauye-sauye ga yadda ake gudanar da tsarin bankuna a kasar, kamar yadda wani sabon rahoto ya bada shawara.

Za a yi garambawul a kan tsarin bankunan ne da nufin hana afkuwar matsalar da aka fuskanta a shekarar 2008, a lokacin da ala-tilas gwamnatin kasar ta zuba dumbin kudade domin ceto wasu bankuna.

Sabbin shawarwarin sun hada da tilastawa cibiyoyin harkokin kudi da su bambanta aikace aikacen da suke baiwa jama'a da harkokin kasuwanci da kuma sauran aikace aikacensu na zuba jari wadanda suke cike kasada.