Erdogan ya na kasar Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mista Erdogan

Firayim Ministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya fara ziyarar kasashen larabawa inda a halin yanzu ya ke kasar Masar.

Zai yi amfani da wannan dama wajen kara neman hanyoyin bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Turkiya da gwamnatin sojin Masar.

Mista Erdogan zai bayyana irin taimakon da gwamnatinsa za ta baiwa kasar Masar, a jawabin da zai gabatar ga kungiyar kasashen Larabawa a birnin Alkahira.

Za a sa ido don ganin ko jawabin nasa zai tabo batun kasar Isra'ila wacce dangantakarta da Turkiya da Masar ta yi tsami.