Jonathan ya nemi a kawo karshen rikicin Filato

Jonathan
Image caption Jonathan lokacin da ya karbi rahoton kwamitin Solomon Lar kan Jos

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya umarci babban hafsan hafsoshin kasar da ya karbe ragamar al'amuran tsaro a jihar Plato domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyar jama'a.

"Ina umartar Air Marshall Oluseyi Petinrin da ya yi duk mai yi wuwa wajen dawo da doka da oda da kawo karshen kashe-kashen da ke afkuwa a Filato," a cewar Jonathan a wata sanarwa da aka aikewa manema labarai.

Matakin da shugaban ya dauka ya biyo bayan ganawar da Majalisar Tsaron kasar ta yi ne a Abuja.

Jonathan ya kuma yumarci sakataren gwamnatin kasar Chief Pius Anyim Pius da ya fito da duk wasu rahotannin kwamitocin baya-bayan nan da gwamnatin tarayya ta kafa kan jihar ta Flato.

'tabbatar da zaman lafiya'

Za a sake duba rahotannin ne domin ganin yadda za a shawo kan rikicin.

"Shugaban ya sake kira kan bangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankali, su kuma tattauna domin ganin an tabbatar da zaman lafiya," a cewar sanarwar.

Ya kuma umarci Hukumar samar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da ta kai dauki ga jama'ar da rikicin ya raba da gidajensu a jihar Filato.

A ranar Talata ne ake saran shugaba Jonathan zai gana da gwamnan jihar ta Filato kan batun.

Jihar ta Filato ta dade tana fama da rikicin da ake alakantawa da addini da kuma kabilanci, inda aka kashe akalla mutane 92 a kwanaki goma da suka wuce.