Ghana ta amince da 'yan tawayen Libya

Shugaba John Atta Mills
Image caption Shugaba John Atta Mills

Ghana ta zama kasa ta baya-baya a nahiyar Afirka da ta amince da majalisar rikon kwaryar Libiya ta NTC.

A wata sanarwa da ta bayar a yau, dauke da sa hannun karamin ministan yada labaran kasar, Samuel Okudzeto Ablakwa, gwamnatin Ghanar ta ce ta dauki matakin amincewa da sabbin mahukuntan Libiyar ne saboda a yanzu gabilin kasar ta Libya tana hannun 'yan tawaye, kuma gwamnatin wucin gadin ta yi alkawarin tabbatar da demokradiyya a cikin kasar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga shugabannin gwamnatin Libyar da su dauki matakan kare baki 'yan Afrika da ke zaune a kasar.