Tsaro: Gwamnatin Filato ta yi raddi

Image caption Jonah Jang

A Najeriya, gwamnatin jihar Filato ta mayar da martani ga matakin da shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya dauka na umartar babban hafsan tsaron kasar ya karbe ragamar tafiyar da tsaron jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Mista Yiljap Abraham, ya shaidawa BBC cewa gwamnan jihar ba zai zama dan kallo game da sha'anin tsaro a jihar ba, kasancewa shi ne babban jami'in tsaro a jihar.

Ya ce a yau Talata ce gwamnan zai nemi karin haske kan manufar shugaban kasar ta mika ragamar tsaron jihar ga babban hafsan tsaron kasar, Air Marshal Oluseyi Petinrin.

A yau din ne dai shugaban Najeriyar zai gana da gwamnan jihar Filato din akan barazanar tsaron da ake fuskanta a jihar.

Jihar Filato dai ta sha fama da rikice-rikice na addini da kabilanci, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.