Goodluck ya gana da Jang

Shugaban Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dr Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya gana da Gwamnan jihar Pilato, Mr Jonah Jang, a kan yadda za a wanzar da zaman lafiya a jihar.

Ganawar ta biyo bayan wani umurni da shugaban kasar ya bayar, na kakkabe hannun gwamnatin jihar Pilaton daga lamuran da suka shafi tsaron jihar, ta hanyar mika aikin tsaron a hannun Babban hafsan tsaron kasar, Air Marshal Oluseyi Petinrin.

Shekaru goma kenan ana fama da rikici mai alaka da kabilanci da siyasa da kuma addini a jihar, wanda ke ci gaba da haddasa asarar rayukan jama`a da dukiya mai dumbin yawa.